– An fara tsere kan wanda zai gaji Shugaban kasa a kasar

– Wata kungiyar Arewa ta kaddamar da neman sahihin dan takara da zai zama shugaban kasa a 2023

– Kungiyar ta kuma bude idonta a kan talauci da rashin tsaro da ke yi wa yankin arewacin Najeriya barazana

Yayinda aka mayar da hankali kan tattauna batun wanda zai gaji shugaban kasa , wata kungiya ta kafa kwamiti domin fara neman sabon shugaban kasa.

Kungiyar arewa, Progressives Movement for Democracy (PDM), ta bayyana hakan a ranar Asabar, 28 ga watan Nuwamba, cewa an ba kwamitin damar samo sahihin dan takara wanda arewa ke gabansa, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Da yake magana a yayin rantsar da kwamitin, shugaban kungiyar, Muhammad Auwal Musa, ya ce arewa ta gaji da zama cibiyar talauci da rashin tsaro a kasar.

2023: Kungiyar arewa ta fara neman magajin Buhari

2023: Kungiyar arewa ta fara neman magajin Buhari Hoto: Bashir Ahmed
Source: Facebook

A cewarsa, manufar kungiyar shine hada kan yan arewa domin ci gaban yankin.

KU KARANTA KUMA: Jam’iyyar PDP na shirin tarwatsewa yayinda karin wasu gwamnoni ke barazanar komawa APC

“Muna son hadin kai domin neman muradin arewa gabannin zabukan 2023, kamar yadda muka yi a 2014 lokacin da aka kafa APC.

“Shugaban kasa zai bar kujerar a matsayin shugaba a 2023. Mun yanke shawarar hada kai da kuma hada yan arewa a karkashin inuwa guda domin mu kawo ci gabanmu hadewarmu a siyasa.

“Dole sai mun yi aiki da nusar da dukkanin jam’iyyun siyasa su gano sahihan yan takara wadanda za su iya wakiltan mutane a dukkan matakai. An tattaro cewa mambobin kwamitin na a fadin jihohin arewa maso yamma.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An kashe mutum 7 tare da kona gidaje a sabon harin Kaduna

A wani labarin, Kingsley Fanwo, kwamishinan labarai da sadarwa na jihar Kogi, ya bayyana cewa Gwamna Bello na fuskantar matsin lamba kan ya fito takarar shugaban kasa a 2023.

Fanwo ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter a ranar Asabar, 28 ga watan Nuwamba.

Sai dai kuma yan Najeriya sun bayyana cewa gwamnan bai isa hawa wannan babban matsayi a kasar ba.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

[embedded content]

Read original article here.