An yi min barazanar kisa a Uganda- Bobi Wine

Wallafawa ranar: 20/11/2020 – 18:20

Magudun ‘yan adawan Uganda Bobi Wine ya ci gaba da nuna turjiya bayan sakin sa daga gidan yari jim kadan da arangamar da magoya bayansa suka yi da jami’an tsaro, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 37.

An gudanar da zanga-zangar kwanaki biyu don nuna adawa da cafke Wine gabanin gangamin yakin neman zabensa, yayin da ake sa ran zai fafata da shugaba a zaben watan Janairu mai zuwa.

A wannan Juma’ar aka tuhumi Wine kan keta ka’idojin takaita bazuwar cutar coronavirus tsakanin jama’arsa da ke halartar manyan tarukan siyasa. Kodayake kotu ta bada belinsa.

A yayin zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP, Wine wanda mawaki ne da ya shiga fagen siyasa ya ce, an azabtar da shi tare da yi masa barazanar kisa a gidan yarin da aka garkame shi.

Sai dai madugun ‘yan adawan ya bayyana cewa, babu abin da zai hana shi ci gaba da fafutukarsa ta nema wa al’ummar Uganda makoma ta gari.

Read original article here.