Jamus za ta sake kulle shaguna saboda korona

Wallafawa ranar: 13/12/2020 – 16:22

Waziriyar Jamus ta shiga tattaunawa da shugabanin yankunan kasar da nufin karfafa matakan da aka dau a baya don hana yaduwar cutar Covid 19 a Jamus.

Ganawar ko kuma tattaunawar ta hanyar bidiyo na zuwa ne bayan da hukumomin kiwon lafiya na kasar suka fitar da alkaluma dake dada nuni cewa an samu karin mutane da suka kamu da kwayar cutar a dan tsakanin nan.

Ana sa ran gwamantin Jamus ta tsananta matakai da za su kai ga rufe shaguna kama daga ranar laraba na mako mai kamawa.

Alkaluman baya-baya daga ranar juma’a zuwa jiya asabar an bayyana kusan mutane 30.000 da suka harbu da kwayar cutar, an kuma bayyana mutuwar kusan mutane 598.

A yau lahadi mutane 20.200 ne suka kamu da kwayar cutar,yayinda 321 suka bakuci lahira a kasar ta Jamus.

Read original article here.