• Daga Massoumeh Torfeh

Sa’o’i 8 da suka wuce

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Bayanan bidiyo,

The road near Tehran where gunmen opened fire on Mohsen Fakhrizadeh

Ga yawancin Iraniya ba su da masaniya har sai ranar Juma’a da aka kashe shi, masanin kimiyyar nukiliyar Iran Mohsen Fakhrizadeh sananne ne ga waɗanda ke bin shirin nukiliyar Iran.

Majiyoyin tsaro na ƙasashen yammaci sun ɗauke shi babban mai tasiri a aikin.

Kafofin yaɗa labaran Iran ba su wani ɗauki Fakhrizadeh da muhimmanci ba, inda suka ɗauke shi kawai a matsayin masanin kimiya mai binciken “kayan gwajin na cutar korona” a makwannin da suka gabata

Mark Fitzpatrick, mai nazari a cibiyar nazari ta Landan da ke bibiyar shirin nukiliyar Iran sosai, ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa: “Shirin nukiliyar Iran ya fi ƙarfin ace ya dogara da mutum ɗaya”

Amma mun san lokacin da aka kai masa hari Fakhrizadeh yana tare da dogarai da yawa, wanda ke nuna girman yadda Iran ke tsaronsa.

Don haka, dalilan kisansa – inda babu wanda ya fito ya yi ikirarin ɗaukar alhaki – zai iya nasaba da siyasa, maimakon abin da ya shafi ayyukan nukiliyar Iran.

Mohsen Fakhrizadeh: Menene dalilan kisan masanin kimiyar na Iran?
Bayanan hoto,

Mohsen Fakhrizadeh, shi ne jagoran bincike da ƙirƙire-ƙirkire a ma’aikatar tsaron Iran

Dalilai guda biyu na iya zama: na farko, don yin zagon ƙasa ga danganta tsakanin Iran da sabuwar gwamnatin Biden ta Amurka. Na biyu kuma, don takalar Iran ta fusata ta yi wani abu na ramuwar gayya.

“Maƙiya na fuskantar damuwa tsawon makwanni ,” in ji shugaba a cikin jawabinsa kan kisan.

Ya ƙara da cewa: “Suna damu cewa yanayin duniya na sauyawa, kuma suna ƙoƙarin yin amfani da waɗannan ranakun don ƙirƙirar wani yanayi marar kyau a yankin.”

Lokacin da Rouhani yake magana kan “maƙiyan” Iran, yana magana ne kan gwamnatin Trump, da Isra’ila da kuma Saudiyya.

Dukkanin Isra’ila da Saudiyya sun damu da sauyin yanayin siyasa a Gabas Ta Tsakiya da kuma abin da zai biyo baya da zarar zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Amurka Joe Biden ya karɓi mulki.

Mista Biden ya fayyace lokacin yaƙin neman zaɓensa cewa yana fatan sake komawa yarjejeniyar nukiliyar Iran, da gwamnatin Barack Obama ya ƙulla a 2015, wacce kuma Trump ta fice a 2018.

Mohsen Fakhrizadeh: Menene dalilan kisan masanin kimiyar na Iran?
Bayanan hoto,

Fakhrizadeh ya ji mummunan rauni a harin kafin daga baya ya mutu a asibiti, kamar yadda jami’ai suka ce

Rahotanni sun ce an tattauna damuwar da Isra’ila da Saudiyya ke da ita game da Iran inda kafafen yaɗa labaran Isra’ila suka ce an yi wata ganawar sirri tsakanin Firaministan Isra’ila da kuma Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammad bin Salman a ranar Lahadi. Amma ma’aikatar harakokin wajen Saudiyya ta musanta cewa an yi ganawar.

Rahotanni sun kuma ce Mista Netanyahu ya gaza shawo kan yariman kan farfaɗo da huldar ƙasashen biyu.

A ranar Litinin, lokacin da mayaƙan Houthi na Yemen da ke samun goyon bayan Iran suka kai hari wata cibiyar man kamfanin Aramco na Saudiyya a birnin Jeddah, batun sake tunkarar Saudiyya bai taso ba.

Kafofin ƴada labaran Iran sun nuna jin daɗinsu da harin makami mai linzami da ƴan Houthi suka kai.

“Yunƙuri ne da ya yi daidai da tattaunawar Saudiyya da Isra’ila, kuma gargaɗi kada su raina su,” a cewar kamfanin dillacin labarai na Mehr.

Amurkawa sun taya Saudiyya jimamin harin.

Tsohon mai bada shawara kan sha’anin tsaro na Amurka, John Bolton a cikin littafinsa, The Room Where It Happened, ya bayyana yadda gwamnatin Trump ta ɗauki goyon bayan Iran ga ƴan Houthi a matsayin “ɗa’awar ƙiyayya ga manufar Amurka a gabas ta tsakiya.”

Rahoton tattaunawar Neom da aka yi an bayyana cewa sakataren harakokin wajen Amurka Mike Pompeo ne ya shirya ta, wanda ya tafi Qatar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, inda batun Iran ne ya mamaye.

Tun makwanni biyu baya, Shugaba Trump ya nemi shawarar manyan masu ba shi shawara ko yana da damar yin amfani da ƙarfin soji ya afkawa cibiyar nukiliyar Iran, kamar yadda kafofin yaɗa labaran Amurka suka ruwaito.

Trump na neman hanyar da yin fito-na-fito da Iran kafin ya sauka.

A watan Janairu, Trump ya yi alfahari kan kisan gillar da aka yi wa babban kwamandan sojan Iran Janar Qasem Soleimani a wani harin jirgin yaƙin Amurka marar matuƙi a Iraƙi, duk da cewa Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana kisan a matsayin wanda ya saɓa doka.

“Mun dakatar da shi da sauri kuma mun dakatar da shi cikin ruwan sanyi.. bisa umurni na,” in ji shi.

Don haka, ana iya cewa, shugaban bai soki kashe-kashen gillar ba dukkaninsu.

Takwaransa na Iran, ya zargi Isra’ila da kisan Fakhrizadeh.

Haka kuma, rahotanni da dama sun bayyana cewa, Firaminista Netanyahu yana ɗaya daga cikin shugabannin duniya da suka yi magana kai-tsaye game da masanin kimiyar.

A wani jawabin da ya gabatar ta kafar talabijin a 2018, ya ambato Fakhrizadeh a matsayin wanda ke jagorantar shirin nukiliyar Iran, tare da cewa mutane su “riƙe sunan kada su manta.”

Yayin da kuma Isra’ila ke da tabbacin cewa Amurka za ta ci gaba da tabbatar da manufarta kan tsaro ƙarƙashin jagorancin Biden, dole kuma ta damu kan wanda ya zaɓa a matsayin sakataren harakokin wajensa Antony Blinken, babban mai goyon bayan yarjejeniyar nukiliyar Iran.

Ana ganin naɗin Mista Blinken dama ce ga Falasɗinawa. Babban mai adawa ne da matakin Trump na ɗauke ofishin jekadancin Isra’ila daga Tel Aviv zuwa birnin Ƙudus. Ko da yake Biden ya ce ba zai sauya ba.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Bayanan bidiyo,

Students of Iran’s Basij paramilitary force rallied in front of the foreign ministry in Tehran

Jagoran juyin juya halin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya yi kiran “hukunci mai tsauri” ga duk masu hannu a kisan Fakhrizadeh.

Shugaban majalisar ƙoli, Mohsen Rezaei, ya ɗora laifin kisan masanin kimiyar ga gazawar tsaro da bayanan sirri.

“Dole hukumomin leƙen asiri su gano masu leƙen asiri na ƙasashen waje, da kuma muƙushe yunkurin kisa,” in ji shi

Iraniyawa da yawa a kafofin sadarwa na Intanet sun ta jefa alamar tambaya kan ta yaya hakan ke faruwa duk da iƙirarin Iran na ƙarfin soji da leƙen asiri, wani zai aikata kisa. Akwai kuma damuwa da ake bayyanawa kan kisan zai iya haddasa kama mutane a cikin ƙasar.

Yanzu da gwamnatin Trump ke kan hanyar ficewa, Isra’ila da Saudiyya za su rasa babban amini. Iran kuma na diba yiyuwar janye mata takunkumi a gwamnatin Biden da kuma fatan sake gina tattalin arzikinta.

Saboda haka, ba zai kasance tunani mai kyau ba na zaɓar yin ramuwar gayya.

Dr Massoumeh Torfeh mai bincike ce a cibiyar nazarin tattalin arziki da ke London (LSE) da kuma cibiyar nazarin al’adun Afrika (SOAS), wadda ƙwararriyar masaniyar siyasar Iran da Afghanistan da Asiya ta tsakiya. Tsohuwar jami’a ce ta Majalisar Ɗinkin Duniya a Afghanistan.

Read original article here.