27 Nuwamba 2020

Mohsen Fakhrizadeh: An kashe babban masanin nukiliyar Iran a Tehran
Bayanan hoto,

Natanz ita ce kadai tashar makamashin uranium Iran wadda aka amince ta yi aiki a dokar kasashen duniya kan yarjejeniyar nukiliya ta shekarar 2015

Ma’aikatar tsaron Iran ta tabbatar da kisan babban masanin nukiliyar kasar Mohsen Fakhrizadeha kusa da babban birnin kasar Tehran.

Fakhrizadeh ya mutu ne a asibiti bayan harin da aka kai a Absard da ke yankin Damavand.

Minista harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif, ya tabbatar da kisan wanda ya bayyana a matsayin “kisan ta’addanci na kasashen waje”.

Jami’an leken asirin kasashen Yammacin Duniya na kallon Fakhrizadeh a matsayin mutumin da yake da ruwa da tsaki a shirin Iran na kera makamashin nukiliya.

Rahotanni sun ce jami’an difilomasiyya suna bayyana shi a matsayin “baban bama-baman Iran”.

Labarin kisan nasa na zuwa ne a yayin da ake nuna sabuwar fargaba kan yadda Iran take kara samar da makamashin uranium. Samar da karin uranium na da muhimmanci wajen samar da makamashin nukiliya da kuma makamin na nukiliya.

Iran ta dage cewa ba wai tana yin shirinta na samar da makamashin nukiliya ba ne domin kai hare-hare.

Mene ne ya faru?

A sanarwar da ta fitar ranar Juma’a, ma’aikatar tsaron Iran ta ce ” Wasu ‘yan ta’adda dauke da makamai sun hari motar da ke dauke da Mohsen Fakhrizadeh, shugaban fannin bincike da tsare-tsare na ma’aikatar.”

“Bayan dauki ba dadi tsakanin ‘yan ta’addan da masu tsaron lafiyarsa, Mr Fakhrizadeh ya samu munanan raunuka inda aka garzaya da shi asibiti.

“Abin takaici shi ne, yunkurin likitoci na ceto rayuwarsa ya ci tura kuma a mintuna kadan da suka wuce ya mutu.”

Kafafen watsa labaran Iran sun ruwaito cewa maharan sun bude wuta kan motar masanin kimiyyar nukiliyar.

Tun da farko rahotanni sun ce an samu fashewar wani abu a garin Absard town, abin da ganau suka ce ya yi sanadin mutuwar “mutum uku ko hudu, wadanda aka ce ‘yan ta’adda ne”.

Wane ne Mohsen Fakhrizadeh?

Mohsen Fakhrizadeh: An kashe babban masanin nukiliyar Iran a Tehran
Bayanan hoto,

Fakrizadeh ya ji mummunan rauni a yayin harin inda aka garzaya da shi asibiti kuma a can ya mutu, in ji gwamnatin Iran

Fakhrizadeh shi ne fitaccen masanin nukiliyar Iran kuma babban jami’i a rundunar dakarun juyin-juya-hali a kasar.

Majiyoyin hukumomin leken asirin Yammacin duniya sun bayyana shi a matsayin mutum mai matukar karfin fada-a-ji wanda kuma shi ne kashin bayan shirin kasar na kera makamai.

Wasu takardu n sirri da Isra’ila ta samu a 2018, sun bayyana cewa shi ne ya jagoranci shirin samar da makaman nukiliyar Iran.

“Na tuna wannan sunan,” a cewar Firaiministan Isra’ila a yayin da yake ya tuna sunan Fakhrizedeh a matsayin shugaban da ya jagoranci kera makamashin nukiliyar iran.

Read original article here.