20 Nuwamba 2020

Promised Land: Kallon da Obama yake yi wa Putin da saura shugabannin ƙasashen duniya
Bayanan hoto,

Barack Obama ya bayyana a matsayin jajuitacce mai ƙwarewa a rayuwa kuma mara son rai

Tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya kwatanta shugaban Rasha a matsayin jajirtacce “kuma uban gida a siyasa” ya kuma bayyana tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy a matsayin “mai yawan cika baki da zuzuta abubuwa” a kashin farko na littafinsa mai kashi biyu.

An sayar da kusan bugu 890,000 na littafin da aka yi wa suna (Promise Land) a Amurka da Canada cikin kwana ɗaya – wannnan wani babban tarihi ne ga kamfanin buga ɗab’i na Penguin Random House.

Ana zaton wannan littafi zai fi ko wanne littafi da wani shugaban ƙasa ya taɓa rubutawa samun kasuwa a tarihi.

A littafin, Mista Obama ya yi tsokaci kan tafiyarsa da ya yi a duniya a matsayinsa na shugaban Amurka 44, da kuma yadda ya riƙa haɗuwa da shugabannin duniya. Su wane ne suka burge shi da saɓanin hakan?

David Cameron

Wanda ya yi karatu a kwalejin Eton ya kuma yi Firaiministan Burtaniya tsakanin 2010-2016 “Wayayyen mutum ne mai kuma ƙwarin gwiwa” kuma mutum ne ” da al’amuran rayuwa ba sa tayar masa da hankali”.

Obama ya ce, ya matukar ƙara min ƙarfin gwiwa (“Ya matuƙar birge ni, ko a lokacin da aka hamaɓarar da shi”) bai kuma ɓoye komai ba game da gaskiyar koma bayan da manufofinsa kan tattalin arziƙin kasar suka janyo.

“Cameron yana tallata aƙidar kasuwancin jari-hujja, alƙawuran da ya yi na kyautata rayuwar al’umma ta hanyar tsuke bakin aljihun gwamnati, tare da sabbin tare-tsaren gwamnati na kasuwanci – wanda hakan zai buɗe kofar gogayya a kasuwanci.”

Promised Land: Kallon da Obama yake yi wa Putin da saura shugabannin ƙasashen duniya

Mista Obama ya ce shugaban Putin na Rasha ya tuna masa manyan masu faɗa a ji na siyasa da ya fara takara da su a Chicago. Ya rubuta cewa “shi kamar wani jigo ne a siyasa”.

Ya ci gaba da cewa, “Putin ya tuna mani wasu mazaje a fagen siyasa da suka tafiyar da Chicago ko in ce ɗakin taro na Tammany a New York, jajirtacce ne, mai ƙwarewa a rayuwa, maras son kansa.

“Irin mutanen nan ne da suka san me suke yi, waɗanda ba su fiye yin katsalanda cikin abubuwan da babu ruwansu ba, wadanda suke kallon cin hanci, da ƙarya da zamba cikin aminci da rikice-rikice da ake samu a matsayin wani halastaccen kasuwanci.”

Nicolas Sarkozy

Promised Land: Kallon da Obama yake yi wa Putin da saura shugabannin ƙasashen duniya
Bayanan hoto,

Barack Obama ya ce yana son yadda Nicolas Sarkozy yake al’amuransa ba shayi

Tsohon shugaban ƙasar Faransa “mutum ne da ke bayyana duk abun da ke ransa kuma mai kwakwazo” in ji Obama.

“Tattanawa da Sarkozy ta zama abin mamaki sai dai kuma akwai ƙularwa, yadda yake yi wa mai yi masa tafinta abin sai wanda ya gani…… yana son ganinsa a ko wanne lokaci a gefensa domin fassara duk wani motsi da ya yi daga na yawo zuwa ɓatanci da shugaban ke yi.

“Yana da wuya ya ɓoye muradinsa, wanda kullum yake sanya wa a gaba, tare da ɗaukar alhakin ko mene ne ya faru da ya kamata ya ɗauki alhakinsa.”

Ya bayyana shugabar gwamnatin Jamus a matsayin “nutsattsiya mai amana mai kaifin basira kuma mai kamun kai.

Ya ce ya lura ta yi ta yin ɗari-ɗari da shi a karon farko. Saboda iya maganarsa da kuma ƙwarewarsa wajen hikimar zance.

“Ban damu ba, da na yi tunanin cewa a zamanta na Shugabar Jamusawa, nuna ƙyama ga yiwuwar wasa da hankalin al’umma abu ne da ya dace”.

Promised Land: Kallon da Obama yake yi wa Putin da saura shugabannin ƙasashen duniya
Bayanan hoto,

Barack Obama ya bayyana a matsayin mace “mai amana da mutunci”

Recep Tayyip Erdogan

Obama ya ce shugaban Turkiyya mutum ne da ke da “kyakkyawar alaƙa kuma mai amsa masa buƙatunsa”.

“Duk lokacin da nake sauraronsa yana magana, yadda yake magana da gudanar da ayyukansa ya nuna yana da jajirtaccen mayar da hankali kan dimokraɗiyya da kuma tabbatar da doka da oda da za su ɗauki dogon lokaci har barin kujerar iko.”

Manmohan Singh

Ya siffanta tsohon firaiministan a matsayin “wayayyen mutum, mai kyakkyawan tunani mai amana” kuma wanda ya jagoranci sauyin tattalin arzikin ƙasar Indiya”.

Mista Singh na da kamun kai yana gudanar da gwamnati da ƙarfin ilimin da yake da shi, ya samu goyon bayan mutane ba ta hanyar roƙonsu ba sai ta yadda ya kyautata lamura da kuma ƙauracewa cin hanci da rashawa,” in ji Obama.

Promised Land: Kallon da Obama yake yi wa Putin da saura shugabannin ƙasashen duniya
Bayanan hoto,

Littafin Promised Land na Obama ya yi farin jini a tun ranakun farko na fitowarsa

Read original article here.